ABNA24 : Shugaban kamfanin hada magungunan na Sino-Farm Lio Jiang ya kuma kara da cewa; Maganin za a rika amfani da shi ne sau biyu a tsakanin sa’o’i, 28, kuma kudinsa zai kama dalar Amurka 140
Jiang ya kuma kara da cewa; Dalibai da ma’aikata da suke a cikin birane za su bukaci a yi musu allufar-rigakafin,amma ba wadanda suke a cikin karkara ba.
Bugu da kari, jiang ya ce; Kamfanin nasu yana da karfin da zai iya samar da maganin rika-kafin na corona da ya kai miliyan 220 a kowace shekara.
Wasu rahotannin daga kasar China sun ce tuni an fara yi wa shugabanni da ma’aikatan kamfanin na kasar Sin, allurar-riga-kafin cutar ta corona.
342/